Rashin yin allurar riga-kafi ya haifar da bazuwar Korona a Indonesiya

Rashin yin allurar riga-kafi ya haifar da bazuwar Korona a Indonesiya

Kwayar cutar Korona ta kara kamari a kasar Indonesiya inda a halin yanzu ake samun kusan mutum dubu 38 dake kamuwa da cutar a rana.

Hakan ya biyo bayan yaduwar sabuwar nau'in cutar ta Delta a yankin da mafi yawanci basu samu yin allurar riga-kafin Korona ba.

Har ila yau, yawan mutanen dake mutuwa  a kowace rana ya kasance 852 yawa mai firgitarwa, adadi na biyu mafi girma a tarihi, yana kara haifar da tsoron cewa ci gaba da yaduwar kwayar cutar na iya mamaye tsarin kiwon lafiyar na Indonesia.

Jimillar sabbin masu dauke da ita a rana na dubu 38,391 ya sanya jumlar yawan wadanda ke dauke da cutar ya fice miliyan 2.41, gami da mace-mace 63,760, a cewar bayanan da rundunar ta COVID-19 ta kasar ta fitar.

Adadin marasa lafiyar da ke karkashin kulawa da kuma mutanen da ke kebe a halin yanzu sun kai 359,000, yayin da wadamnda suka warke ya kai miliyan biyu inda ake samun masu warkewa kusan dubu 22 a rana.

Indonesiya na ta kokarin yin kokarin hana yaduwar kwayar cutar, tare da sanya dokar tsaurara matakai a cikin tsibirin Java da Bali mafi yawan mutane daga ranar 3 ga Yuli zuwa 20 ga Yulin.


News Source:   ()