Ana fargaban cewa rashin abinci da rashin muhalli zai shafi fiye da rabin al'umman kasar Amurka.
Dangane ga binciken da kanfanin binciken Allup ta gudanar, kaso 55 cikin darin Amurka na cikin fargaban zasu rasa muhalli da kuma fuskantar matsalar rashin abinci. Wannan dai zai kasance mafi yawa a cikin shekaru 20 da suka gabata.
Yawan wadanda ke cikin fargaban rasa mazauna da kuma fuskantar yunwa ya karu da kaso 8 cikin dari a shekarar 2020 da Korona ta fara addabar duniya.
Haka kuma shakku game da tattalin arzikin kasar ya karu da maki 16 inda ya kai 49 cikin dari.
'Ya'yan jamiyyar Republican sun fi shakku game da yiwuwar bunkasar tattalin arzikin kasar inda mutum kaso 58 cikin dari ke shakkun hakan, 'yan jamiyyar Democrat kuwa kason mutum 40 cikin dari keda shakku game da bunkasar tattalin arzikin kasar.