Sanarwar da fadar ta fitar, ta ce shugaban ɗariƙar ta Katolika na duniya Fafaroma Francis zai ci gaba da zama a Asibiti ba tare da sanar da tsawon lokacin da zai ɗauka ba, sakamakon tarin na bronchitis wanda ciwon hunhu ke haddasawa.
Cikin ayyukan Fafaroma da fadar ta Vatican ta soke har da manyan tarukan addini biyu da aka tsara za su gudana a ƙarshen mako inda fadar ke cewa zai ci gaba da karɓar kulawa kan tarin na bronchitis a asibiti.
Ko a makon jiya Fafaroma mai shekaru 88 bai halarci taron addu’ar tsakar-rana ta Angelus a Lahadin da ta gabata ba, sai dai a wannan karon fadar ta Vatican ta ce an wakilta wani babban fada don jagorantar addu’o’in safiyar Lahadin ba tare da ambato waɗanda bisa ƙa’ida aka saba gudanarwa da tsakar-rana ba.
Fafaroma Francis yana ci gaba da samun kulawa a asibirin Gamelli na cikin Rome, inda bayanai ke cewa zai iya ɗaukar tsawon lokaci fiye da yadda aka tsara zamanshi a asibitin.
Jagoran na ɗariƙar ta Katolika daya hau kujerar tun a shekarar 2013, tsawon lokaci ya shafe yana fama da jinyar matsalolin lafiya da dama, inda a wannan karon aka garzaya da shi asibiti bayan sarƙewar lumfashin da ya kai ga ya gaza karanta jawabin addu’o’insa a bainar jama’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI