Rashin kayan aiki da tallafin noma ka iya haifar da rashin abinci a Afirka

Rashin kayan aiki da tallafin noma ka iya haifar da rashin abinci a Afirka

Matsanancin karancin kayan aiki da rashin tallafi ga noma da bangarorin abinci a Afirka na iya haifar da karancin abinci da kuma kawo cikas ga ci gaban kasashe a fadin nahiyar, in ji shugaban harkokin noma na Majalisar Dinkin Duniya.

Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da Asusun Jama'a na Kungiyar Abinci da Aikin Gona (FAO) a Saharar Afirka, Babban Daraktan FAO QU Dongyu ya ce dole ne a fadada asusun noma kuma a inganta tsarin kudaden jama'a  domin yin aikin noman cikin sauki.

Ya kara da cewa,

"Bari mu toshe matsalolin da ke kawo cikas ta hanyar habaka aikin noma tare da haɓaka kwarewar ɗan adam a cikin ƙasashen Afirka,"

Ya jaddada cewa hakan ne zai bunkasa harkokin noma da zai sanya a samar da wadataccen abinci a nahiyar.

 


News Source:   ()