Rasha ta yi ruwan makamai masu linzami a Ukraine a ranar Kirsimeti

Rasha ta yi ruwan makamai masu linzami a Ukraine a ranar Kirsimeti

Harin ya raunata a ƙalla mutum 6 a arewacin Kharkiv tare da kashe mutum guda a yankin Dnipropetrovsk  kamar yadda gwamnan yankin ya tabbatar.

Kusan shekara 3 kenan ana fafata yaƙi tsakanin ƙasashen.

Kusan mutane dubu 500 ne aka bari a Kharkiv babu ababen jin ɗumi yayin da suke cikin yanayin tsananin sanyi da ya kai kusan ma’aunin celsius 0, babu kuma hasken lantarki a birnin Kyiv da wasu wurare a ƙasar.

Udakarun sojin Ukraine sun ce na’urorin tsaron sararin samaniyarsu sun kakkaɓo makamai masu linzami 59 na Rasha.  

Galibin mutanen Ukraine Kiristocin Orthodox ne, sun kuma amince a shekarar 2023 su fice daga tsarin kalandar Julian ta Rasha da suke bikin Kirsimetinsu a ranar 7 ga watan Janairu.

Rasha ta matsa da kai hare-hare a wuraren makamashin Ukraine tun a tsakanin watan Maris da watan Mayu inda ta lalata kusan rabin wuraren dake samarwa da ƙasar lantarki abinda ya jefa sassa da dama ciki duhu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)