Harin, idan aka tabbatar da shi, zai nuna yadda tankiya ke kara ta’azzara a wannan yaƙin da aka shafe watanni 33 ana gwabzawa, bayan da ita ma Ukraine ta harba makami mai linzami da ta samu daga Amurka da Birtaniya cikin Rasha a wannan makon, duk da kashedin da Rasha ta sha yi.
Ƙwararru a fannin tsaro sun ce zai kasance karon farko da aka yi amfani da makami mai linzami da ke cin dogon zango, makamin da aka ƙera don harba makaman nukiliya zuwa nesa, kuma ya ke wani ɓangare mai mahimmanci na shirin nukiliyar Rasha.
A wani saƙon bidiyo, shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce, gudu da tasirin wannan makami ya nuna cewa Rasha ta harba makami mai linzami mai cin dogon zango, wanda a Turance ake kira ‘intercontinental ballistic missile’.
Rundunar sojin saman Ukraine ta cikin wata sanarwa, ta ce an harba makamin ne daga yankin Astrakhan na Rasha, mai nisan kilomita 700 daga Dnipro na tsakiya maso gabashin Ukraine. Sai dai ba ta yi bayani ko makamin na ɗauke da nukiliya ba.
Da aka tambaye shi a kan sanarwar sojin saman Ukraine, kakakin fadar Kremlin, Dmitry Peskov ya tura manema labarai gun rundunar sojin Ukraine don amsar da su ke nema.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI