Mutane bakwai suka jikkata yayin da wani guda ya rasa ransa sakamakon hare-haren da Rashan ta kai kan babban birnin na Ukraine da safiyar yau.
Ma’aikatar harkokin wajen Ukraine ta ce hare-haren na Rasha sun kuma lalata ofishohin jakadancin ƙasashen ketare har guda shida dake tsakiyar birnin Kyiv.
Baya ga birnin na Kyiv, Rashan ta kuma hai wasu hare-haren a birnin Kherson inda ta halaka mutum guda da jikkara wasu da dama a dai safiyar ta yau, kamar yadda jami’an Ukraine suka tabbatar.
Cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar tsaron Rasha ta ce hare-haren na ɗaukar fansa ne kan farmakiin da Ukraine ta kai kan wata babbar cibiyar sarrafa sinadaran ƙasar ta hanyar amfani da makamai masu linzamin da kasashen yammacin Turai ke taimaka mata da su.
A iya cewa dai ga dukkanin alamu tsugunno ba zai ƙare ba a nan kusa, domin a wannan Juma’a kungiyar Tarayyar Turai EU ta sanar da shirin bai wa Ukraine tallafin kuɗi na dala biliyan 36 duk dai saboda yakinta da Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI