Rasha ta kashe sojojin Ukraine kusan 300 tare da kwace yankin Kursk a hannunsu

Rasha ta kashe sojojin Ukraine kusan 300 tare da kwace yankin Kursk a hannunsu

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha sanar da cewa, dakarunta sun lalata tankar yaki guda daya, jirgin yaki, da kuma motocin yaki guda hudu.

“A yau kadai, Ukraine ta yi asarar sojojinta sama da 290, da kuma wata tankar yaki, jirgin yaki, hadi da motocin yaki guda hudu.

Ma'aikatar ta kara da cewa, yawan hasarar da Ukraine ta yi a yankin Kursk tun bayan fara yakin, ya kai kimanin mayaka 50,120, da tankokin yaki 294, da motocin yaki 217.

Kasashen Korea ta Kudu da Amurka sun yi zargin cewa, shugaba Kim Jong Un na Korea ta Arewa, ya jibge sojoji sama da dubu 10 a Kursk, inda aka kasha daruruwa daga cikinsu.

Duk da cewa Rasha na fama da karancin tankoki da motocin yaki, amma rahotanni na cewa tana ci gaba da fadada mamayarta a Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)