Rasha ta harbo jirage marasa matuka na Ukraine 47

Rasha ta harbo jirage marasa matuka na Ukraine 47

Sanarwar dakarun na Rasha na zuwa a wani lokaci da Shugaban na Rasha Vladmir Poutine ya dau alkawarin mayar da martani mai zafi  tare da yin amfani da duk wasu makamai da Rasha ke da su mudin Ukraine ta malaki makamin nukiliya.

Wasu daga cikin hare-haren da Rasha ta kai yankunan Ukraine Wasu daga cikin hare-haren da Rasha ta kai yankunan Ukraine AP - Francisco Seco

 Rahotanni daga majiyoyin tsaron Rasha na nuni da cewa dakarun kare sarrarin samaniya na Rasha sun lalata jiragen sama marasa matuka na Ukraine guda 47," ciki har da jiragen sama 29 a yankin Rostov dake kudancin kasar.

A cikin wannan yanki, wata babbar gobara ta tashi a kan "wata masana'anta" a gundumar Kamensky, kuma an aika da ma'aikatan kashe gobara sama da ɗari a wurin, a cewar gwamnan yankin Yuri Sliosuar wanda ya ba da rahoto a shafin sa na Telegram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)