Sanarwar ta Rasha na zuwa a dai dai lokacin da Mohammed al-Bashir ya karɓi ragamar Syria a matsayin Firaminista bayan hamɓarar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, jagoran da ya samu cikakken goyon bayan ƙasashen Rasha da Iran a tsawon shekaru da ƙasar ta shafe ta na fama da yaƙin basasa, ko da ya ke ya yi takun saƙa da manyan ƙasashe waɗanda sune suka jagoranci yaƙin tsawon shekaru a cikin ƙasar.
Yanzu haka dai tuni ƙasashen Faransa da Jamus suka miƙa wuya bayan bayyana cewa a shirye suke su yi aiki da sabon shugaban ƴan tawayen da ya karɓi ƙasar, matakin da masana alaƙar ƙasashe irin Dr Abdulhakeem Garba Funtua ke cewa dole sabon jagoran Mohammed al-Bashir ya yi taka-tsan-tsan.
A gefe guda Isra’ila na ci gaba da mamayar yankuna a cikin ƙasar ta Syria bayan da a baya-bayan ta sake nanata cewa yankin tuddan golan ya fita daga matsayin wucin gadi ya koma mallakinta na dindindin, batun da kai tsaye ke matsayin koma baya ga Tehran, wadda ke amfani da wani ɓangare na Syria wajen shigar da kayaki Lebanon, ko da ya ke Dr Abdulhakeem ya ce wannan mataki ba zai kassara Tehran ba, face koma baya ga yankin Falasɗinu.
Duniya dai ta zuba ido don ganin abin da ka je ya zo a wannan ƙasa wadda ta faɗa yaƙi tun a watan Maris ɗin shekarar 2011, lokacin da jama'a suka faro bore ga shugaba Assad amma kuma ya yi amfani da ƙarfi wajen murƙushe su, batun da ya haddasa ɓullowar mabanbantan ƙungiyoyin ƴan tawaye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI