A Rasha, an yanke hukuncin daurin shekaru 16 ga wani Ba'amurke Paul Whelan da aka samu da laifin aikata leken asiri.
Kotun Birnin Moscow ta yi zaman karshe tare da yanke hukunci game da zarge-zargen da aka yi wa Paul Whelan.
Kotun ta amince da Whelan ya yi leken asiri a Rasha, sakamakon haka ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 16 a gidan kurkuku.
Lauyan Whelan ya bayyana cewar za su daukaka kara.
Lauyoyin gwamnatin Rasha kuma sun nemi da a daure Whelan na tsawon shekaru 18.
Jakadan Amurka a Rasha John Sullivan ya fadi cewar wannan hukunci abu ne na karya zuciya da bacin rai.
A watan Disamban 2018 ne jami'an tsaro na farin kaya na Rasha suka kama Paul Whelan bia zarginsa da yin leken asiri inda suka kuma kai shi kurkuku.