Rasha ta bayyana Turkiyya a matsayar muhimmiyar abokiyar hulda

Rasha ta bayyana Turkiyya a matsayar muhimmiyar abokiyar hulda

Mataimakin firaiministan Rasha Aleksandr Novak ya bayyana cewa, Turkiyya muhimmiyar kawa ce ga kasarsa.

Novak ya yi jawabi a Taron Kasuwancin Turkiyya da Rasha wanda Hukumar Hulda da Tattalin Arzikin Kasashen Waje ta (DEIK) ta shirya a Moscow, babban birnin Rasha.

da yake sharhi akan alakar da ke tsakanin Rasha da Turkiyya, Novak ya jaddada cewa, alakar kasashen biyu ta kai matsayin "kawance" da "abota".

Da yake lura da cewa kasashen biyu sun fahimci ayyukan hadin gwiwa a fannoni da dama, Aleksandr Novak ya tunatar da cewa, aikin shimfida bututun iskar gas na TurkStream da na Nukiliyar Akkuyu (NGS) an aiwatar da su kamar yadda aka tsara.

Da yaye kuma nuna cewa dangantakar kasuwanci tsakanin Turkiyya da Rasha ta inganta, Novak ya ce,

"Wannan shi ne yanki mafi muhimmanci a ci gaban alakar da ke tsakanin kasashenmu. Turkiyya ta kasance muhimmiyar abokiya ga Rasha dangane da hadin kanmu a fagen kasuwanci da ci gaban ayyukan saka jari. Turkiyya na daga cikin kasashe 7 da Rasha ke tare da su a fannin cinikayya."

Da yake bayyana cewa sama da kamfanonin Turkiyya dubu 3 suna aiki a fannoni daban-daban a Rasha, Novak ya jaddada cewa suna goyon bayan wadannan kamfanonin da ke saka jari a cikin tattalin arzikin Rasha.

Novak ya bayyana cewa, akwai yuwuwar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a bangaren kimiyyar sadarwa, jiragen ruwa da na jiragen sama.


News Source:   ()