Ma'aikatar tsaron kasar ta ce a ranar alhamis sojojinta na ci gaba da ragargaza wasu sassan Ukraine dake dauke da makamai wadda suke amfani dasu wajen kai hare-hare ta sama da roka da manyan bindigogi a kokarin da suke yi na haifar da cikas a duk wani kokari da sojojin Rasha keyi a gwabzawar.
Mukaddashin gwamnan yankin Alexey Smirnov ya ce ya sanar da kafa dokar ta-baci bayan da dakarun da ke goyon bayan Ukraine suka kutsa cikin yankin a ranar Talata, inda suka jibge sojoji kusan 1,000 da motoci masu sulke da tankokin yaki fiye da ashirin da biyu, a cewar sojojin Rasha.
Dama dai shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy a ranar Laraba ya bayyana cewa Idan suka yi karin matsa lamba akan Rasha to za su samu zaman lafiya akasar su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI