Rasha da Uzbekistan za su gudanar da atisaye a kan iyakar Afghanistan

Rasha da Uzbekistan za su gudanar da atisaye a kan iyakar Afghanistan

Rasha da Uzbekistan za su gudanar da atisayen hadin gwiwa a kusa da kan iyakar Uzbekistan da Afghanistan.

An bayyana cewa, atisayen wanda za a gudanar tare da halartar sojoji dubu 1 da 500 da jiragen sama na sojoji kusan 200, za a gudanar da shi tsakanin 30 ga watan Yuli da 10 ga watan Agusta.

Za a gudanar da atisayen hadin gwiwar ne a kusa da garin Surkhandarya da ke kudancin Uzbekistan.

A wata sanarwa da Rundunar sojoji ta Rasha ta fitar a ranar Litinin din nan, an bayyana cewa za a gudanar da wani atisaye a kan iyakar Afghanistan daga 5 zuwa 10 ga watan Agusta tare da halartar Rasha, Uzbekistan da Tajikistan.


News Source:   ()