Ƙasashen na Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunonin yaƙin waɗanda galibinsu sojojine daga kowanne ɓangare a yau litinin. bayan shiga tsakani da Hadaɗɗiyar Daular Larabawa ta yi, kamar yadda hukumomin ƙasashen 2 suka tabbatar.
Ɓangarorin dake yaƙi da juna sun yi musayar ɗaruruwan fursunoni tun bayan ƙaddamar da yakin da Rasha ta yi a Ukraine a watan Fabarairun 2022.
Ma’aikatar tsaro ta Rasha ta ce a ranar 30 ga watan Disambar nan aka cimma yarjejeniyar wadda ta bada damar miƙawa mata sojojinta 150 da Ukraine ta kama, ita ma Ukraine aka miƙa mata sojinta 150.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce ya karɓi mutum 189 a wani ɓangare na yarjejeniyar da aka cimma wanda a cikinsu akwai dakarun soji da masu tsaron iyaka da fararen hula 2 daga Mariupol da Rasha ta mamaye.
Dukkanin ɓangarorin sun tabbatar da cewa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ce ta shiga tsakani wurin cimma wannan musayar fursunonin yaƙi.
Wani bidiyo da Kwamishinan Hukumar Kare Hakkin ɗan Adam ta Rasha Tatyana Moskalkova ya fitar ya nuna yadda sojojin suka taru sanye da kayan sanyi.
Ya kuma godewa dakarun na Rasha bisa hakuri da ƙwarin gwiwa da suka nuna
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI