An ba da rahoton cewa sojojin Rasha da China za su gudanar da atisayen soji na hadin gwiwa a watan gobe.
A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Tsaro ta Rasha ta fitar, an bayyana cewa, wasu rundunoni daga sojojin Rasha za su halarci atisayen soja na "Interaction-2021", wanda za a gudanar a kasar Chına a tsakiyar watan Agusta.
An bayyana cewa kimanin sojoji dubu 10 za su halarci atisayen hadin gwiwar, an kuma jaddawa cewa jiragen sama na sojoji da motoci masu sulke ne za'a yi amfani dasu.
"Manufar atisayen ita ce karfafa huldar dake tsakanin Rasha da China, kawancen hadin gwiwa da mu'amala bisa manyan tsare-tsare, don kara matsayin hadin gwiwa a fannin soja da kawance tsakanin rundunonin sojojin kasashen biyu, don nuna jajircewa da kuma karfin Rasha da China na yaki."