Rasha da China sun ƙarfafa alaƙar tsaro da ƙarfin Soji don tunƙarar matsalolinsu

Rasha da China sun ƙarfafa alaƙar tsaro da ƙarfin Soji don tunƙarar matsalolinsu

Yayin wata ziyara da ministan tsaron Rasha Andrei Belousov ya kai birnin Beijing ɓangarorin biyu sun yi doguwar tattaunawar da ta shafi tsaro da ƙarfin Soji inda suka amince da wata sabuwar yarjejeniyar ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu.

Ministan tsaron na Rasha Andrei Belousov yayin jawabinsa gaban manema labarai a birnin Beijing ya yaba da matakin ƙarfafa alaƙa tsakanin ƙasashen biyu wadda ya ce ba ta tsaya a iya tsaro da ƙarfin Soji ba.

A cewar ministan alaƙa tsakanin Rasha da China za ta ci gaba da ƙarfafuwa ta kowacce fuska ta yadda za ta amfani kowanne sashe da ci gaban ƙasashen biyu.

A ɓangare guda minsitan tsaro na China Admiral Dong Jun ya bayyana cewa ƙasar ta shi a ƙage ta ke ko yaushe wajen ƙarfafa alaƙa tsakaninta da Rasha lura da alfanin hakan ga tsaro da zaman lafiyar yankin.

Ziyarar ta Belousov a Beijing na zuwa ne a wani yanayi da China ke shirin ɗaukar mataki kan yankin Taiwan kwanaki bayan wani atisayen shawagin jirage da ƙasar ta gudanar a gab da yankin.

A baya-bayan nan dai akwai zargin da ke nuna yiwuwar Rasha ta faɗaɗa alaƙar da ke tsakaninta da Korea ta Arewa a wani yanayi da ake ganin Pyongyang na shirin taimakawa Moscow da dakaru na musamman don yi mata yaƙi a Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)