An sanar da cewa Radiyo ne babban abinda al’umma a fadin duniya suka fi amfani dashi wajen sauraren labarai, raye-raye, shirye-shirye da makamantansu.
Radiyo ya kansance abinda al’umma suka yawan saurare a karni na 19 abinda ya baiwa mutane daman jin abubuwan dake faruwa a lokacin yakin duniya na biyu.
Tare da bayyana wasu kafafen yada Labarai dake da alaka da Radiyo kamar su Radiyon yanar gizo, podcast da wayoyin hannun radiyo na cigaba da zama abin sauraro mai muhinmanci a duniya.
Kasancewarsa mara tsada na daya daga cikin abinda ya sanya Radiyo ke cigaba da zama abinda miliyoyin al’umma ke amfani dashi a doron kasa.