Kashi biyu cikin ukun Amurkawa ba sa goyon bayan yakin da kasarsu ta gudanar a kasar Afghanistan.
An bayyana cewa kawonan Amurkawa ya rarrabu kan tsaron kasa da manufofin kasashen wajen mulkin shugaba Joe Biden kuma mafi yawan Amurkawa na tunanin cewa yakin da kasarsu ta yi a Afghanistan bai da muhinmanci, kamar yadda wani binciken hadin gwiwa da kamfanin dillancin labarai na Associated Press (AP) da Cibiyar Binciken Harkokin Jama'a ta NORC ya nuna.
Kusan kashi biyu bisa uku na wadanda suka halarci binciken jin ra'ayin alumma sun ce suna tunanin yakin da Amurka ta kwashe shekaru tana yi a Afganistan "bai cancanci yakin ba."
An kammala binciken da cewa kashi 47 cikin 100 na mahalarta taron sun amince da manufofin dangantakar kasashen waje na Biden sannan kashi 52 daga cikinsu sun amince da manufar tsaron kasarsa"
An gudanar da binciken ne a ranakun 12 zuwa 16 ga watan Agusta, ciki har da ranar da babban birnin kasar Afghanistan, Kabul, ya koma karkashin ikon 'yan Taliban a ranar 15 ga watan Agusta ta kuma karbe ikon kasar, sannan aka kawo karshen yakin shekaru 20 a Afghanistan.
Haka nan kuma jam’iyyun Republican da Democrat sun la’anci gwamnatin Biden saboda haddasa rikicin jin kai a yankin ta hanyar nuna halin ko -in -kula ga ci gaban da Taliban ke samu a kasar.