Shugaban Putin, wanda ke gabatar da jawabi a gaban jami’an Majalisar Tsaron ƙasar a cikin daren jiya, ya ce suna kallon cewa duk wata ƙasa da ke kai hari kan Rasha ko da kuwa ba ta mallaki makamin nukilya ba, matuƙar tana samun taimakon wata ƙasa da ta mallaki irin wannan makami, to a ganinsu tamkar tana kai wa Tarayyar Rasha hari ne.
Shugaban Putin dai bai ambaci sunan Ukraine ba, amma kalamansa na matsayin ishara ne ga irin tallafin makamai da kuɗaɗen da ƙasashen duniya ke bai wa mahukuntan birnin Kiev.
Akwai makamai masu linzami da ke cin dogon zango da ƙasashen da ke ƙarkashin kawancen NATO suka bai wa Ukraine, to sai dai sun gindaya sharaɗin cewa ka da ta yi amfani da su a cikin ƙasar Rasha, yayin da Volodymyr Zelensky ke ganin cewa lokaci ya yi da ya kamata a ba shi damar yin amfani da su don ƙaddamar da farmaki cikin Rasha.
Shugaba Vladimir Putin ya yi gargaɗin cewa muddin suka samu cikakkun bayanai da ke tabbatar da cewa Ukraine za ta ƙaddamar da gagarumin farmaki da makaman da ta karɓar daga NATO har zuwa cikin Rasha, to ko shakka babu zai iya yin amfani da makaman nukilya.
Tun cikin shekarar ta 2023 ne Rasha ta girke manyan makamanta na nukiliya a makociyarta wato Belarus, kuma ko a watan Mayun da ya gabata, sai da ƙasashen biyu da ke maƙotaka da Ukraine suka gudanar da atisayin haɗin-gwiwa a tsakaninsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI