Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tattauna da Shugaban Azabaijan Ilham Aliyev da Firaministan Armeniya Nikol Pashinyan kan abubuwan da suka faru a Nagorno-Karabakh.
A cikin wata sanarwa da Kremlin (Fadar Shugaban Rasha) ta fitar, an bayyana cewa Putin ya tattauna da Aliyev da Pashinyan ta wayar tarho.
Sanarwar ta bayyana cewa an tattauna kan yarjeniyoyin da aka cimma dangane da Nagorno-Karabakh.
An kuma bayyana da gamsuwa cewa an yi aiki da tsarin tsagaita wuta kuma yankin ya kasance cikin halin kwanciyar hankali da nutsuwa baki daya.