Putin ya sanya hannu kan sabuwar dokar amfani da makamin nukiliya

Putin ya sanya hannu kan sabuwar dokar amfani da makamin nukiliya

Matakin dai ya zo ne a rana ta dubu ɗaya da Rasha ta ƙaddamar da hare-hare a Ukraine, da kuma sahalewar da Amurka ta yi wa Kyiv na yin amfani da makamai masu cin dogon zango wajen kai hari cikin Rasha.

Jim kadan bayan sanya hannun da Putin yayi kan sabuwar dokar, kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov, ya shaidawa manema labarai cewa ya zamewa ƙasar wajibi ta faɗaɗa dokokinta na amfani da makamai masu linzami, sakamakon barazanar tsaro da ake yiwa Moscow.

Hari daga ƙasar da bata da makamin nukiya, amma tana samun goyon bayan ƙasar da ke da makamin nukiliya, muna kallonsa a matsayin harin haɗin gwiwa.

Tuni dai babban jami'in difulomasiyyar ƙungiyar Tarayyar Turai EU mai barin gado Josep Borrell ya yaba da matakin na Amurka, tare da matsawa ƙasashe mambobin ƙungiyar lamba a yayin taronsu na yau wanda shi ne na ƙarshe da zai jagoranta, da su bi sahun Amurka wajen baiwa Ukraine damar kai hari cikin Rasha ta hanyar amfani da makami mai linzami da suka bata a matsayin gudunmuwa.

Damar da shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden ya baiwa Ukraine na yin amfani da makamai masu cin dogon zango da ƙasarsa ta bata a matsayin tallafi domin kai hari kai tsaye cikin Rasha, ita ce ta farko tun bayan faro yaƙin da ake yi tsakanin  a shekarar 2022.

Shugaban Ukraine Volodímir Zelenski tare da shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden. Shugaban Ukraine Volodímir Zelenski tare da shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden. REUTERS - Kevin Lamarque

Wani babban jami’in gwamnatin Amruka ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, makaman da Biden ya ba wa Volodymyr Zelenskyy umarnin yin amfani dasu akan Rasha, masu cin zangon kilomita 300 ne.

Kafin matakin na Amurka dai an yi ta samun saɓanin ra’ayi tsakanin shugabanin ƙungiyar Tarayyar Turai game da bai wa Ukraine damar amfani da makamai masu cin dogon zango da suke bata akan Rasha.

Tuni dai gwamnatin Rasha ta zargi shugaban Amurka Joe Biden da ta'azzara yaƙin da ake yi a Ukraine, inda ta yi alƙawarin mayar da martani ga matakin da Biden ya ɗauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)