Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a yayin da ya gudanar da taron kolin majalisar tsaron kasarsa sun tattauna akan maslahar Libiya.
Mai magana da yawun fadar gwamnatin Cremea Dmitriy Peskov, ya sanar da cewa shugaba Putin ya gudanar da taron kolin majalisar gtsaron kasar ta yanar gizo inda ya kara da cewa an tattauna akan yadda za’a samar da lumana a Libiya.
Peskov ya kara da cewa a taron kuma an tabo batutuwan yankin Balkan da kuma Yukiren.