Shugaban kasar rasha Vladimir Putin, da shuagaban kasar Azabaijan Ilham Aliyev da na Armeniya Nikol Pashiyan zasu tattauna a birnin Moscow gobe.
Kamar yadda fadar gwamnatin Rasha ta sanar sanadiyar shiga tsakanin Putin a ranar 11 ga watan Janairu 2021 da halartar Putin din shugabanin uku da suka hada da Aliyev da Pashinyan zasu tattauna gobe a Moscow.
A taron za'a tatttauna akan lamrin Nagorno Karabakh da aka kubutar, a ranar 9 ga watan Nuwamba 2020 aka kuma yi yarjejniyar zaman lafiya da kuma hanyoyin da za'a bi domin magance matsalolin yankin.
Bayan zaman shugabanin uku Putin zai gana da Aliyev da Pashinyan daban-daban.
Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan samar da kayan agaji ga wadanda ke zaune a yankunan da ake fama da rikice-rikice, tare da kauda dukkan kalubale tare da bunkasa shingayen kasuwanci, tattalin arziki da hanyoyin sufuri.