A cewar shugaba Pezeshkian ko kaɗan Iran ba ta taɓa tunanin hallaka Trump ba, kuma ba za ta taɓa irin wannan tunani ba.
Yayin wata hirarsa da tashar NBC shugaba Pezeshkian ya nanata cewa shirin nukiliyar ba komai ya ke ƙunshe da shi ba face zaman lafiya ya na mai gargaɗin cewa Trump na da shirin kawo yaƙi ga duniya.
Tattaunawar ta shugaba Pezeshkian wanda ake yiwa kallo a matsayin mai tsaka-tsakan ra’ayi na zuwa ne ƙasa da mako guda gabanin rantsar da shugaba Donald Trump na Amurka, a wani yanayi da ake tsoron jagoran na Washington ya bijiro da wasu manufofi da za su sake wargaza alaƙarsa da Tehran.
Cikin watan Nuwamban bara ne ma’aikatar tsaron Amurka ta tuhumi wani ɗan Iran da hannu a yunƙurin kisan Trump yayin harin da aka kai masa, mutumin da kai tsaye aka alaƙanta shi da dakarun juyin juya halin Iran.
Ka zalika shi da kansa Donald Trump ya bayyana cewa akwai yiwuwar Iran na da hannu a yunƙurin kisan shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI