Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na Musamman kan Siriya Pedersen ya bayyana cewar yakin basasar da aka kwashe shekaru 10 ana yi a Siriya yana matsayin wani shafi mai duhu a tarihi kuma Siriyawa ne wadanda abun ya fi shafa a wannan karnin.
Da yake sanar da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya game da abubuwan da ke faruwa a Siriya, Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na Musamman kan Siriya Geir Pedersen ya ce wannan bala'in na shekaru 10 "ya kasance tsawon Yakin Duniya na biyu" kuma ana bukatar sabon tsarin kasa da kasa na diflomasiyya don warwarewa rikicin.
Da yake bayyana cewa Siriyawa sun fuskanci mutuwa, nakasa, azabtarwa, yunwa, yin hijira da kuma hatsari daga makamai masu guba a yayin wannan lamarin, Pedersen ya jaddada cewa yana matukar bakin ciki cewa Majalisar Dinkin Duniya ba za ta iya kawo karshen wannan mummunan rikicin ba.