Paparoma zai ziyarci jagoran shi’a a Iraki Ali Sistani

Paparoma zai ziyarci jagoran shi’a a Iraki Ali Sistani

Paparoma Francis zai gana da wani babban malamin Shi’a Ayatollah Ali Sistani a ziyarar farko da zai kai a kasar Iraki a watan Maris.

Wani jami’in Katolika ne ya shaidawa kanfanin dillancin labaran France-Presse kamar yadda shugaban Katolika na Iraki Loius Sako ya bayyana cewa ganawar za a yi tane a bayan fage a gidan Sistani da ake kira Najaf.

Sistani, mai shekaru 90, bai cika bayyana a waje ba kuma bai cika karbar baki ba. Amma ganawar da zai yi da Paparoma ta zo ne bayan wasu jami’an darikar Katolika sun ziyarci kasar ta Iraki.

Sako ya kara da cewa shugabanin biyu zasu rataba hannu akan hulda da juna, domin zaman lafiya a doron kasa da kuma nuna kyama ga tsattsaurar ra’ayi.

Paparoma Francis ya rataba hannu akan irin wannan manufar da daya daga cikin shugabanin Sunni Sheikh Ahmed al-Tayeb, babban limamin Al-Azhar, a watan Febrairun shekarar 2019.


News Source:   ()