Shugaban darikar Katolika, Paparoma Francis ya halarci taron da aka gudanar a Fiilin wasa na Franso Hariri da ke garin Erbil na Iraki.
A rana ta uku da ziyararsa Iraki, Paparoman ya tashi daga Erbil zuwa Mosul inda ya je da safe kuma ya halarci ibadun da ake gudanarwa a tsakiyar gari da kuma gundumar Karakus, sannan ya koma Erbil da rana.
Bayan da Paparoman ya gaisa da jama’ar da suka taru a bakin titi a Unguwar Aynkava da ke Erbil inda Kiristoci suka fi yawa sai ya ziyarci Filin wasan Franso Hariri.
A filin wasan inda kusan mutane dubu 10 suka hallara, an rera wakoki wa Paparoman wanda ya gaisa da mahalarta taron.
Shugaban Gwamnatin Yankin Kurdistan (KRG) Nechirvan Barzani, Firaminista Masrour Barzani, Mataimakin Firaminista Kubat Talabani, Wakilin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a Iraki Jeanine Hennis, jami'an diflomasiyya na yankin, jami'an addini da kuma jami'an gwamnati sun halarci taron da aka gudanar a filin wasan.
Da yake jawabi a wajen taron, Paparoman ya ja hankali game da tasirin yaki da tashe-tashen hankali a kan mutane da yawa a Iraki tare da yin kira ga Kiristoci su zauna cikin 'yan uwantaka, hidima da jin kai.
Da yake nuna godiyar sa ga majami’u da tushoshin da suka goyi bayan sake gina Iraki, shugaban darikar Katolika ya nuna cewa son daukar fansa ne ya sanya kasar fadawa cikin wani yanayi na tashin hankali.