Shugaban kwamitin majalisar dokokin Pakistan a kan Kashmir ya zargi Indiya da yin kwatankwacin tsarin mamayar da Isra’ila ke aikatawa a Gaza a yankin a Jammu da Kashmir da ke karkashin ikonta.
Shehryar Khan Afridi, wanda ya yi jawabi a wajen wani taron karawa juna sani a Islamabad babban birnin kasar, ya ce dole ne duniya ta tashi tsaye don tinkarar ta'addancin Indiya a yankin da take mamaya.
Afridi ya ce "Kafin 5 ga watan Agusta, 2019, gwamnatin Indiya ta aika da manyan 'yan sanda da ma'aikatan gwamnati dake aiki a Jammu da Kashmir zuwa Isra'ila don koyo, horo sannan kuma suka dawo da su don sake kwaikwayon samfurin Isra'ila a Jammu da Kashmir."
"Daga cikin wadanda Indiya ta aika Isra'ila har da wani dan sanda mara mutrunci Imtiaz Hussain, wanda ake zargi da kisan Musulman Kashmiri 200. An aika Imtiaz Hussain zuwa Isra'ila don fahimtar tsarin tsaron Isra'ila kafin 5 ga watan Agusta, 2019, kuma bayan dawowa, an sanya shi a matsayin tsaro a- caji a Srinagar don murƙushe zanga-zangar a Jammu da Kashmir."