Pakistan ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta tuhumi Indiya kan leken asiri da na'urar Pegasus
Pakistan ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta yi “ cikakken bincike” game da yaduwar amfani da manhajar Pegasus da Isra’ila ta kirkira don leken asiri kan ‘yan jarida, masu kare hakkin dan Adam,‘ yan siyasa, da sauransu.
"Ku bayyanar da hujjojin gaskiya, kuma ku tuhumi wadanda suka aikata laifin a Indiya," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan a cikin wata sanarwa, tana magana ne kan amfani da kayan leken asiri na Isra'ila da Indiya ta yi.
"Mun lura da matukar damuwa da rahotannin kafofin watsa labarai na duniya na baya-bayan nan da ke fallasa ayyukan leken asirin da gwamnatin Indiya ta shirya a kan 'yan kasarta,' yan kasashen waje da firaiminista Imran Khan, ta hanyar amfani da wani na'urar leken asiri na Isra'ila"
Ya kara da cewa "Mun yi Allah wadai da kakkausar murya akan amfani da na'urar leken asirin da Indiya ke yi, lamarin da ya sabawa dokokin kasa da kasa"