Firaiministan Pakistan Imran Han ya bayyana cewa rikicin dake tsakanin Iran da Saudiyya ya kai makura mafi muni a yankin.
Imran Han, ya shaidawa kafar talabijin din Aljazeera ta kasar Kuwait da cewa kasar na daukar wasu matakai game da gabsa ta Tsakiyya.
Inda ya bayyana cewa "Yankin na cikin hali mafi muni sabili da Iran da Saudiyya na kusa da fara rikici kai tsaye a tsakaninsu"
Han ya tabbatar da cewa Pakistan na yunkurin kare afkuwar hakan.
Ya kara da cewa "Muna shiga tsakanin Tahran da Riyad sai dai hakan na tafiyar hawainiya"
Han ya kuma yi sharhi akan Musulmin Indiya dake fuskantar nuna wariya,
"Indiya na yiwa Musulmin kasar kamar yadda NAzi a Jamus suka yi wa Yahudawa"
Shugaban ya kara da cewa suna daukar matakan samar da lumana a yankin kasarsa dsa Turkiyya kuma na kara daukar bunkasa tattalin arzikin dake tsakaninsu.