Kasar Pakistan ta karyata shaci-fadin da ake yadawa dake nuna cewa sojojin kasarta na taya sojojin Azerbaijan yakar na Armeniya akan yankin Nagorno-Karabakh.
Ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta bayyana cewa irin wannan zargi ne wanda bai da tushe; bai da kan gado da ake yadawa domin tada zaune tsaye.
Ma’aikatar ta kara jaddada matsayinta akan lamarin inda ta kara bayyna damuwar da kasar Pakistan ke yi akan rikicin yankin Nagorno-Karabakh. Inda ta kara da cewa,
“Mamayar da Armeniya ke yiwa yankin da farar hular Azerbaijan ke zama abin kalubalanta ne kuma abin bakin ciki. Wannan lamari ne da zai ci gaba da dakile zaman lafiyar yankin. Ya zama wajibi ga Armeniya da ta dakatar da hare-haren sojin da take kaiwa domin gujewa barkewar babban rikici a yankin”