Omer Celik da Kungiyar Yahudawa Turkawa sun mayar da martani ga Amurka

Omer Celik da Kungiyar Yahudawa Turkawa sun mayar da martani ga Amurka

Kakakin Jam'iyyar Adalci da Ci gaba, Omer Celik ya bayyana cewa Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta yi kakkausar suka ga kalaman Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na Twitter, da Celik ke bayyana cewa zargin shugaba Erdogan da kyamar Yahudawa ya nuna rashin hankali kuma bai dace ba ya ce,

"Wannan karya ce aka fada game da shugaban kasar mu." 

Da yake jaddada cewa Shugaba Erdogan yana kuma yana ci gaba da yin kakkausar suka ga kyamar Yahudawa, Celik ya jaddada cewa ba zai yiwu ba ga wadanda ke goyon bayan takurar da gwamnatin Netanyahu a Isra'ila ke yi su rufe gazawar lamirinsu ta hanyar yin karya kan Erdogan.

Al’umar Yahudawa Turkawa ma sun mayar da martani game da ikirarin da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta yi cewa shugaba Erdogan ya yi amfani da kalaman nuna kyamar Yahudawa.

A cikin sanarwar da aka fitar a shafukan sada zumunta na Kungiyar Yahudawa Turkawa an bayyana cewa,

"Rashin adalci ne kuma abun kunya ne a ce shugaba Erdogan ya nuna kyama ga Yahudawa. Akasin haka, ya kasance yana taimaka mana, yana ba mu goyon baya da karfafa mana gwiwa."


News Source:   ()