Omar ta sake samun damar takarar majalisar Amurka a karo na 4

Omar ta sake samun damar takarar majalisar Amurka a karo na 4

Omar ta kada Don Samuel domin samun tikitin mazabar Minnesota na 5. Rahotanni sun ce tun daga shekarar 2022 'yar majalisar ke samun gudumawar kudin domin tsayawa takarar wadanda suka kai dala miliyan 6 da dubu 800.

Omar na daga cikin 'yan majalisun dimokrat da suka yi ta takun saka da tsohon shugaba Donald Trump lokacin da yake jagorancin kasar a kan wasu manufofinsa na cikin gida da kasashen ketare, musamman abinda ya shafi Isra'ila da Falasdinu.

A watan Nuwamba mai zuwa ne ake saran gudanar da zaben shugaban kasar Amurka da na 'yan majalisu, wanda ake hasashen zai yi zafi a wannan karon saboda yunkurin tsohon shugaban kasa Donald Trump na sake dawowa karagar mulki.

Sai dai wasu masu sanya ido na bayyana cewar ficewar shugaba Joe Biden da shigar mataimakiyarsa Kamala Harris na iya sauya sakamakon zaben mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)