Mataimakin shugaban kasar Turkiyya, Fuat Oktay ya taya kasar Kazakhstan murnar bukin "Ranar Samun 'Yanci".
Kazakhstan ta samu ‘yancin kai a ranar 16 ga watan Disamban 1991 bayan rugujewar Tarayyar Soviet.
Oktay, a sakon da ya yada a shafinsa na sada zumunta ya bayyana cewar,
"Ina taya abokanmu da 'yan uwanmu 'yan kasar Kazakhstan murnar Ranar Samun 'Yanci. Shekaru 29 da suka gabata, a lokacin da Kazakhstan suka sanar da samun 'yancin kan kasarsu ita ce kasa ta farko da ta amince da Turkiyya. Hadin kan da muke da ita kan alakar tarihi da al'adu za su ci gaba da karfafa ta kowane bangare."