Okonjo-Iweala: Ya zama wajibi a wadata kasashe masu tasowa da allurar rigakafin korona

Okonjo-Iweala: Ya zama wajibi a wadata kasashe masu tasowa da allurar rigakafin korona

Babban Daraktan Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana cewa ya zama wajibi ga kanfunan da suka sarrafa allurar rigakafin korona su wadatar da kasashe masu tasowa da allurar ko kuma su kai kayan kimiyya da fasaha a kasashen domin sarrafa allurar. 

Okonjo-Iweala, da take bada misali ga hadakar da kanfanin  AstraZeneca ta yi da Cibiyar Serum dake lndiya ta bayyana cewa babu wadatattun alluran da zaa yi amfani dasu a kasashe masu tasowa. 

 Ta kuma kara da cewa ba za a saka ido a kyale kasashe masu tasowa da rashin allurar rigakafin korona ba. Wannan ba abinda da zaa yi shiru akansa ba ne.

Sabili da haka ya zama wajibi ga kanfunan da suka sarrafa allurar rigakafin korona su wadatar da kasashe masu tasowa da allurar ko kuma su kai kayan kimiyya da fasaha a kasashen domin sarrafa allurar. 

Okonjo-Iweala, da take yabawa aikin hadin gwiwar da kanfanin AtraZeneca ta yi a Indiya ta bayyana cewa ya kamata sauran kanfuna kamarsu  "Novovax, Johnson & Johnson su yi koyi da hakan.

 


News Source:   ()