Yayin zantawa da manema labarai karon farko tun bayan wannan rashin nasara mai muni, Ten Hag ya ce ya kamata jama’a su san shi ba matsafi bane ta yadda zai iya kawar da rashin nasara idan ta zo.
A yanzu haka dai Ten Hag na cikin tsaka mai wuya tun bayan rashin nasara da ya fara yi a gasar ta Premier league da aka fara bugawa, da kuma rashin nasara kan Brighton a makon da ya wuce.
Ko a kakar da ta gabata ma Ten Hag bai wani tabuka abin a zo a gani ba, kasancewar ƙungiyar tasa ta ƙare ne a mataki na 8, to amma hakan bai sa ya rasa aikin sa ba, kamar yadda aka saba gani da sauran kwacha-kwachai.
Duk da rashin tabuka abin a zo a gani din tsohon kocin na ƙungiyar Ajax Hag ya sake tsawaita kwantaraginsa da ƙungiyar da kuma kashe Yuro miliyan 200 wajen cefano sabbin ƴan wasa, amma hakan bai hana Liverpool yin kacha-kacha da su ba.
Ten Hag ya ce yanzu ne aka fara kakar, kuma yana da matasan ƴan wasa da bai ma fara sanya su a fili ba, don haka yana da yakinin cewa Liverpool ta ciyo mai ƴaƴa, ma’ana dai zai tabbatar da ya doke duk ƙungiyar da yayi karo da ita.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI