Netherlands za ta mayarwa Najeriya kayayyakinta na tarihi sama da 100

Sanarwar da ofishin jakadancin Netherlands a Najeriya, ya fitar ta ce, Ministan raya Al'adu, na kasar, Eppo Bruins, da Darakta Janar na Hukumar Kula da Gidajen Tarihi ta Najeriya, Olugbile Holloway, sun sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Laraba.

Najeriya na ci gaba da ƙoƙarin ganin ta samu dubban kayyakin tarihinta, musamman na tagulla da aka sarrafa, waɗanda sojojin Birtaniya suka wawashe a wani samame da suka kai wa Masarautar Benin da ke yankin kudu maso yammacin kasar, a shekarar 1897.

Kayayyakin tarihin, ana sa ran za su isa ƙasar ne a ƙarshen wannan shekarar, kamar yadda sanarwar ta tabbatar.

Ƙasar ta ce matakin zai taimaka wajen wanke laifukan da aka aikatawa Najeriya, musamman a bangaren da suka danganci kayayyakin tarihi da sauransu, da kuma sake gyara alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)