A lokacin da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa Falasdinawa hare-hare, Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya yi kalaman da suka kara ruwa wutar rikicin.
Ya ce, "Muna tsakiyar yaki kuma za mu ci gaba da kai hare-hare da dukkan karfinmu."
Netanyahu ya gudanar da taro tare da Ministan Tsaro Benny Gantz, Babban Hafsan Rundunar Sojin Isra'ila Aviv Kochav da sauran shugabannin sojin kasar.
Firaminista Netanyahu ya bayyana cewa, "Za su dandana kudarsu", wato yana nufin kungiyar Hamas dake mayar da martani ga hare-haren zalunci na Isra'ila da makaman roka inda ya kara da cewar, "yakin" zai dauki lokaci ba a daina ba.
Ya ce, "Za mu tabbatar da tsaron jama'ar Isra'ila".
Netanyahu ya kuma ce, za su ci gaba da kai hare-haren cikin sauri.
Ministan Tsaro na Isra'ila Gantz kuma ya bayyana cewa, ba a ga komai ba, wadannan hare-hare somin tabi ne suka kaiwa Zirin Gaza.
Kungiyoyin Fafutuka na Zirin Gaza da suka baiwa 'yan sandan Isra'ila wa'adin su janye daga mamayar da suka yiwa Masallacin Aksa da unguwar Shaikh Jarrah ne suka harba makaman roka zuwa Isra'ila tare da kashe Yahudawa 5.
Sakamakon haka Isra'ila ta fara kai farmakan "Masu Tsaron Katanga" a Zirin Gaza.