Tuni Netanyahu ya maye gurbin Gallant da tsohon ministan harkokin waje Israel Katz, matakin da ya haifar da gagarumar zanga zanga a Birnin Tel Aviv.
Safiyar yau Talata sojojin Isra'ila sun bai wa mazauna arewacin Gaza umarnin janyewa daga yankin tare da kuma kai hare haren sama a kan jami'an kula da lafiya da 'yan jaridu, abinda ya kai ga hallaka mutane 35.
Netanyahu ya kuma nada Gideon Saar a matsayin sabon ministan harkokin wajen kasar kamar yadda ofishinsa ya sanar.
Rahotanni sun ce an kwashe makwanni ana takun saka tsakanin Netanyahu da Gallant wadanda suka fito jam'iyyar Likud saboda muhimmancin yakin da suka kwashe watanni 13 suna yi a Gaza domin murkushe mayakan Hamas.
Netanyahu ya zargi Gallant da yin wasu kalamai wadanda ya ce sun sabawa manufofin gwamnatinsa, ya yin da Gallant ya jaddada cewar tsaron Isra'ila zai ci gaba da zama ginshikin rayuwarsa.
Ana saran ministan harkokin wajen Faransa ya ziyarci Isra'ilar gobe Laraba domin matsin lamba ga gwamnatin kasar domin kawo karshen yakin da take yi a Gaza da Lebanon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI