Netanyahu ya gana da Biden kan yaƙin Gabas ta Tsakiya

Netanyahu ya gana da Biden kan yaƙin Gabas ta Tsakiya

Ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fitar da sanarwa lokacin da aka fara tattaunawa tsakanin shugaba Joe Biden da Netanyahun, ba tare da bayani a kan abinda shugabannin ke tattaunawa a kai ba.

Sai dai gabanin fara wayar, an bayyana cewar tataunawar shugabannin biyu za ta mayar da hankali ne akan yakin da Israila ta kwashe shekara guda tana yi da kungiyar Hamas da yadda yakin ya fantsama zuwa kasashen Lebanon da Yemen da Syria da kuma Iran.

Rahotanni sun ce daga cikin abinda shugabannin za su tattauna harda harin ramakon da Isra'ila za ta kai wa Iran na ramako, sai dai an ce akwai banbancin ra'ayi a tsakanin shugabannin biyu dangane da wannan hari.

Yayin da Netanyahu ke shirin afkawa cibiyoyin kasar Iran daban daban, Biden na ganin akwai wasu cibiyoyin da ya dace ayi taka tsan tsan wajen kai harin, wadanda suka hada da cibiyoyin nukiliyar Iran da kuma rijiyoyin man ta.

Wasu bayanai sun ce Netanyahun ya ki amincewa da gayyatar ministan tsaronsa zuwa Amurka domin tattauwa dangane da shirin kai harin, abinda wasu ke cewa na nuna barakar da ake samu tsakanin bangarorin biyu.

Netanyahu yace babu abinda zai hana su kai hari Iran, kuma kasarsa ba zata taba barin Iran ta mallaki makamin nukiliya ba saboda yadda ta hakikance cewar sai ta ga bayan ta a doran kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)