Nau’in kwayar cutar Korona ta Delta ta yi kamari a Jamus

Nau’in kwayar cutar Korona ta Delta ta yi kamari a Jamus

Nau'in kwayar cutar Korona ta Delta mai saurin yaduwa ya kama kashi 85 cikin darin wadanda suka kamu da cutar Korona a fadin kasar Jamus.

Nau'in Korona na Delta bai wuce kashi 2 cikin dari ba daga cikin wadanda ake samu da cutar a watan Mayu,  amma ya yadu cikin sauri a duk fadin kasar, inda ya zarta wasu nau'ikan kwayar ta corona a cikin kankanin lokaci, a cewar Cibiyar Robert Koch.

A makon farko na watan Yuni, ya kai kusan kashi 8 cikin dari na sabbin kamuwa da cutar a Jamus, amma Deltan ya ninka sau biyu a kowane mako, inda ya kai zuwa kaso 60 cikin dari na wadanda ake samu dauke da cutar a wajan jiya.

Rahoton kwanan nan ya nuna cewa nau'in Delta ya karu zuwa 84 cikin dari a wannan watan, bisa ga sabon bayanan da aka samu kan sa ido kan kwayoyin halittar.

An fara gano nau'in cutar Korona ta Delta a Indiya a shekarar da ta gabata, kuma ya na yaduwa sau 60 fiye da sauran kwayoyin cutan.


News Source:   ()