An bayyana cewa nau'in Delta na sabon nau'in coronavirus (Kovid-19) ya mamaye duniya.
Rochelle Walensky, Darakta a Cibiyoyin Kula da Rigakafin Cututtuka a Amurka, ta sanar da cewa cutar ta Kovid-19 a kasar ta karu da kashi 70 da kuma mace-mace da kashi 26 cikin 100 idan aka kwatanta da makon da ya gabata.
Walensky ta bayyana cewa cutar ta karu a yankunan kasar dake da karancin adadin wadanda suka yi allurar riga-kafi.
Anthony Fauci, babban masanin cututtukan a Amurka, ya ce an ga nau'in Korona na Delta a kasashe kusan 100 a duniya, lamarin dake nuna kamarin da cutar ya yi a doron kasa.
Dangane da bayanai daga Cibiyoyin Kula da Rigakafin Cututtuka, adadin yawan wadanda ke kamuwa da cutar a cikin kwana bakwai a Amurka yanzu ya fi 26,000.
Wannan ya ninka ninki biyu na karancin yawan masu cutar da aka samu a watan Yuni na 11,000.
Ya zuwa yanzu, mutane 608,828 sun mutu daga Kovid-19 a fadin kasar.