Turkiyya da Girka zasu zauna akan teburin sulhu domin tattaunawa akan harkokin da kasashen biyu ke muhawara akai.
A jiya ne dai aka yi niyar zaman amma an dage zaman har zuwa ranar 10 ga watan Satumba.
Kamar yadda ma'aikatar harkokin tsaron kasar Turkiyya ta sanar bayan tattaunawar shugaban kasar Turkıyya Recep Tayyip Erdoğan da sakatare janar na NATO Jens Stoltenberg ne aka shirya zaman tawagar dakarun kasar Turkiyya dana Girka a hedikwatar NATO.
A taron da za'a gudanar da hedikwatar NATO wanda za'a tattauna akan "Hanyoyin Rabe-raben iyakoki", shugaban harkokin gudanarwar sojin kungiyar NATO ya dage shi zuwa 10 ga Satumba.