Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg ya yiwa Turkiyya, Amurka da Birtaniya godiya akan samar da tsaro a Afganistan.
Stoltenberg ya bayyana cewa,
"Ina mika godiya ta musamman ga Turkiyya, Amurka da Birtaniya saboda muhimmiyar rawar da suka taka wajen tabbatar da tsaron filin jirgin sama a Kabul."
Ministocin harkokin waje na kasashe membobin kungiyar tsaro ta NATO sun gudanar da wani taro na musamman ta yanar gizo akan ajandar Afghanistan.
Da yake bayani bayan taron, Stoltenberg ya bayyana cewa idanun duniya na kan Afghanistan,
"Ba za mu sake barin kungiyoyin 'yan ta'adda su sake yin gida a yankin ba. Muna aiki don kwashe mutane a awanni 24 a rana ba tare da katsewa ba. Turkiyya na taka muhimmiyar rawa. Muna godiya da hakan."
Da yake bayyana cewa ra'ayin kowa daga dukkan abokan kawance shi ne Taliban ta cika alkawarinta, Stoltenberg ya kara da cewa,
"Ko mu a matsayinmu na NATO za mu kulla alakar diflomasiyya da sabuwar gwamnatin idan ta cika alkawurran da ta yi"
Da suka killace babban birnin Kabul a ranar Lahadin da ta gabata, 'yan Taliban sun karbe ikon birnin ba tare da rikici ba yayin da shugaba Ashraf Ghani ya bar kasar yayin da sojojin gwamnati suka bar babban birnin.