Kungiyar NATO ta yi kira ga kasashen Azerbaijan da Armeniya dasu dakatar da rikice-rikicen da suke yi akan iyakokin dake tsakaninsu.
Wakilin babban sakataren NATO Jens Stoltenberg a Caucasia da Asiya ta Tsakiya James Appathurai, ya fitar da wata sanarwa a rubuce inda ya bayyana cewa NATO na matukar damuwa akan rikicin da kasashen biyu ke tafkawa a iyakokin Nagorno-Karabakh.
A yayinda Appathurai ke baiyana cewa ana samun hasarar rayukan farar hula a rikicin ya yi kira ga kasashen biyu dasu mayar da takubansu kobe nan take.
Haka kuma a yayinda yake bayyana cewa matakin soja ba zai taba kawo karshen rikicin ba ya kara da cewa,
"Dukkanin bangarorin ya zama wajibi dasu zauna akan teburin sulhu. NATO da Kungiyar Minsk ta Tarayyar Samar da Zaman Lafiya a Turai zata taimakawa zaman sulhun kasashen biyu"
Rikici ya yi kamari ne tsakanin bangarorin biyu bayan sojojin Armeniya sun kaiwa sansanin sojan Azerbaijan hari a yankin.