Nasarar Trump za ta jefa tattalin arzikin duniya cikin rashin tabbas - Rahoto

Nasarar Trump za ta jefa tattalin arzikin duniya cikin rashin tabbas - Rahoto

Masana tattalin arziki sun ce, matakan Trump na sanya harajin akalla kashi 60 cikin 100 kan kayayyakin da China ke shigarwa cikin kasar da kuma harajin kashi 10 zuwa 20 cikin 100 kan duk wasu kayayyaki na kasashen waje, za su kara nauyin harajin zuwa matakan da ba a taba gani ba.

Yayin da Trump ya dora harajin dala biliyan 380 na kayayyakin da Amurka ke shigo da su daga China, shawarwarin da ya gabatar a wannan karon za su shafi kayayyakin da darajarsu ta ninka sau 10.

Donald Trump, daga hagu, lokacin da yake yin musabaha da shugaban China Xi Jinping yayin wata ganawa da suka yi a gefen taron kungiyar G-20 da ya gudana a Osaka, dake yammacin Japan, ranar 29 ga Yuni, 2019. Donald Trump, daga hagu, lokacin da yake yin musabaha da shugaban China Xi Jinping yayin wata ganawa da suka yi a gefen taron kungiyar G-20 da ya gudana a Osaka, dake yammacin Japan, ranar 29 ga Yuni, 2019. AP - Susan Walsh

Habakar tattalin arzikin duniya masana suka ce akwai alamar zai iya fuskantar sarkakiya, yayin da ake ganin ‘yan kasuwa na iya rage sayen kayayyakin ketare, musamman idan kasashe suka sanya harajin ramuwar gayya kan kayayyakin da aka sayo daga Amurka.

Bankin UBS na kasar Switzerland ya yi kiyasin cewa, karin harajin kashi 60 cikin 100 kan kayayyakin kasar China da kuma karin harajin kashi 10 cikin 100 ga duniya zai rage karuwar tattalin arzikin duniya da kashi daya cikin dari a shekarar 2026.

Tambarin da ke jikin bankin UBS na kasar Switzerland kenan a birnin Zurich Tambarin da ke jikin bankin UBS na kasar Switzerland kenan a birnin Zurich REUTERS - Denis Balibouse

Wani bincike da kwararru a kwalejin nazarin tattalin arziki da kimiyyar siyasa ta Landan ta yi, ya yi hasashen samun raguwar tattalin arzikin China da kasa da digo daya, haka zalika akwai fargabar faruwar hakan ga kasashen mambobin Kunbgiyar Tarayyar Turai shima da kasa da kaso guda.

Rahoton binciken ya kuma ce, kasashen India, Indonesia da Brazil, suma akwai fargabar za su fuskanci saukar tattalin arzikinsu a ma’aunin GDP da kaso guda.

Idan aka yi la’akari da yadda Trump ya aiwatar da manufofinsa a baya, hasashen kwalejin ya ce, yana da wuya a iya hasashen yadda zai aiwatar da manufofin da suka danganci haraji.

A lokacin yakin neman zabensa, ya bayyana haraji a matsayin kalmar da ya fi so kuma a cewarsa mafi kyawun kalma a cikin littafin Kamus.

A watan Satumba, Trump ya yi barazana ga wani kamfani da ke sarrafa kayan gona, cewar zai caje shi harajin kashi 200 cikin dari idan har ya koma Mexico.

A watan da ya gabata ma na Oktoba, ya yi alkawarin fitar da motocin China da aka kera a Mexico daga Amurka, yana mai cewa zai sanya duk wani harajin da ake bukata kama daga kaso 100, 200, har zuwa 1000.

Wani taron gangami da Donald Trump ya halarta, wanda kungiyoyin masu tsatssauran ra'ayi suka shirya a Las Vegas, ranar 24 ga Oktoba, 2024. Wani taron gangami da Donald Trump ya halarta, wanda kungiyoyin masu tsatssauran ra'ayi suka shirya a Las Vegas, ranar 24 ga Oktoba, 2024. © Carlos Barria / Reuters

Ana ganin manufofin Trump da suka danganci tattalin arziki ka iya haifar da illa ga kasashe masu karfin tattalin arziki.

Binciken da masanan suka yi ya yi hasashen cewa, akwai alamun dalar Amurka za ta kara karfi daidai lokacin da ake fama da hauhawar farashin kaya, kuma ana ganin baitul malin kasar zai rubanya kudin ruwa ga wadanda yake bi basuka.

Daga lokacin da dala kuma ta tashi, akwai kasashen da za su fuskanci karyewar darajar kudadensu, wanda hakan zai iya kara kudin da ake kashewa wajen shigar da kayayyaki.

Idan har dala ta kara karfi kuwa, masana tattalin arziki suka ce hakan zai karawa wasu gwamnatocin nauyi, musamman wajen sauke basukan da ake binsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)