Hukumar sararin samaniyya ta kasar Amurka watau NASA ta bayyana cewa zata tura 'yan sama jannati biyu daya na miji daya na mace a duniyar wata a shekarar 2024.
Kamar yadda NASA ta bayyana akan wata shiri mai suna "Artemis" a shekarar 2024 za'a tura masana sararin samaniyya biyu zuwa duniyar wata.
Shugaban gudanarwar NASA Jim Bridenstine ya bayyana cewa akwai bukatar dala biliyan 28 domin tura masanan zuwa duniyar wata karkashin shirin Artremis bayan shekaru hudu.
Ana dai shirin aikawa da 'yan saman jannatin ne da jirgin rocket wanda zai yi amfani da na'urar SLS akan kampasa din Orion.