Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Amurka (NASA) ta yada hotunan da tauraron dan adam ya dauka na gobarar dain da ta kama a Turkiyya.
Hotunan sun bayyana yadda ake yaki da gobarar dajin ba kakkautawa.
NASA ta yada hotunan Antalya da tauraron dan adam na Landsat 8 ya dauka.
Ta sanar da cewa, tsawon mako guda gobarar daji na ci a Turkiyya,gobara 130 ta kama inda daga ranar 3 ga Agusta 9 na ci gaba da ci.
NASA ta ce, gobarar dajin da ta kama a Gabas ta Tsakiya da Turai, ta fara ci a Girka.