NASA ta yada bidiyon saukar kumbon "Perseverance" a duniyar Mars

NASA ta yada bidiyon saukar kumbon "Perseverance" a duniyar Mars

Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Amurka (NASA) ta yada bidiyon saukar kumbon "Perseverance"mai bincike a duniyar Mars.

Sanarwar da aka fitar daga shafin Twitter da NASA ta bude don bayar da bayanai game da Perseverance ta bayyana hotuna da bidiyon yadda kumbon ya sauka a duniyar Mars a ranar Asabar din karshen makon da ya gabata.

Bidiyon ya fara da budewar lemar tashi sama wadda ta nuna yadda kumbon ya rage sauri a lokacinda ya shiga duniyar Mars, an kuma ga yadda kumbon ya sauka daram a duniyar ta Mars.

An samu nasarar saukar kamar yadda aka tsara a cibiyar NASA.

A ranar 30 ga watan Yunin 2020 ne aka harba kumbon Perseverance daga cibiyar harba makaman roka da ke Florida, kuma bayan watanni 7 da tafiyar kilomita miliyan 470 ya sauka a duniyar Marsa a ranar 20 ga Fabrairu.


News Source:   ()